Ba Za’a Samu Cigaba a Kasar Nan ba Sai an Hada Kai da Juna – Sanata Ahmad Lawan

 

Sanata Ahmad Lawan ya ce akwai wasu dabi’un da ya kamata masu rike da mukaman shugabanci a Najeriya su mallaka.

Shugaban majalisan dattawan ya bayyana wannan ra’ayin ne yayin gabatar da jawabi a kwalejin tsaron Najeriya, Abuja.

Lawan ya ce akwai bukatar hadin kai na gaske tsakanin yan Najeriya Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya lissafa abubuwa hudu da ya kamata duk wani shugaba a Najeriya ya mallaka.

Lawan, wanda dan majalisa ne daga Yobe ya bayyana wadannan dabi’u yayin gabatar da jawabi a Kwaljin tsaron tarayya dake Abuja.

Hadiminsa na sabbin kafafen yada labarai, Abubakar Sadiq Usman, ya bayyana abinda maigidansa ya fada ranar 2 ga Febrairu, 2021.

A cewar shugaban majalisar dattawan, kowani shugaba na kwarai yana bukatan:

1. Ikon karfafa cigabar kasa

2. Ikon cika burukan mutane

3. Shirya sauraron mutane, da daukan mataki

4. Barin tarihi na kwarai ga yaran gobe

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa ba za’a samu cigaba a kasar nan ba sai an hada kai da juna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here