CIGABA (II) AKAN SANYA ANKLET KO CHAINS A KAFA; A Mahangar Kimiyar Zamantakewar Dan Adam “Sociology” 

 

Cigaba da bayani akan fahimtar makarantar “Symbolic interactionism” da kuma nazarin Erving Goffman akan “Tie sings”

Kamar yadda Goffman yace; Tie signs wasu alamomi ne da suke dauke da ma’ana ko suke son isar da wani sako. Saboda haka Tie signs sun hada da zobe, sarka ko anklet.

Haka kamar yadda muka fahimci ita wannan makarantar gabadaya tayi ikirarin cewa ; Ana fahimtar dan Adam wajen mu’amalar yau da kullum, dakuma isar da sako ta hanyar “nonverbal means” ma’ana batare da yafadi wani abu ba ko yayi wani furuci, non verbal din sune Symbols, da sauran gestures, ko mosti da gabobin jiki.

SHIN SANYA SARKA, CHAINS KO ANKLET KWALLIYA KO WATA MA’ANA?

Kamar yadda mukai bayani a baya, cewa; “Ana iya fahimtar Dan Adam wajen isar da sako ta hanyar nuni da kuma wata alama dayake dauke da ita”.

Wannan yana nufin duk wata alama tana dauke da ma’anarta. Dukda cewa ana samun yanayin dawani zai amfani da wata alama, kuma baisan ma’anar ta ba. Misali; a shekarun baya mutane suna daukar hoto kansu akasa, ko su sauke hannunsu xuwa kasa, kansu kuma yakalli gefe, abunda ake kira “daff”.

Wasu kuma suna daga yatsun hannun su guda 2 su danne sauran idan zasu dauki hoto a matsayin “Wiskid style” ammma a hakikanin fahimtar “symbolism” wadannan abubuwan ko styles akwai wata ma’ana da suke dauke da ita. Koda kuwa wanda yayi baisan ma’anar su ba, yana wuya ya tsira da tuhuma ko zargin wadannan abubuwan da yayi tozali dasu.

Kamar haka, sanya Anklet, chains ko Sarka, yana da ma’ana iri daban-daban. Daga cikin ma’anar sune kamar haka:

1- Domin kawata ado ko “fashion” fashio

2- Domin jingina kai da wata kungiya, ko alaqanta kai da wata dabi’a.

3- Ana sakawa domin koyi da wasu al’adu wajen yanayin kwalliyarsu.

A dakacemu…. Domin, zamu cigaba daga inda muka tsaya.

Marubucin:Sameen Y Saeed (Dr.SYS) Masanin Zamantakewar Dan Adam, kuma me fashin baki akan al’amuran yau da kullum. Yana rubutawa daga Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here