Yau Za’a Cigaba da Sauraron Shari’ar El-zazzaky da Matarsa

A yau, 18 ga watan Nuwamba ne za a cigaba da sauraron shari’ar El-Zakzaky da matarsa.

Idan ba a manta ba, suna hannun hukuma tun watan Disamban 2015, bayan rikicin kungiyar da sojoji.

Dama an dage sauraron shari’ar ne bayan kotu ta ki amincewa da bayar da Belinsa, a ranar 5 ga watan Augusta A yau 18 ga watan Nuwamba ake cigaba da sauraron shari’ar El-Zakzaky a Kaduna, kamar yadda gidan talabijin din Channels suka ruwaito.

Dama kotu ta ce za ta cigaba da duban yuwuwar bayar da belin El-Zakzaky wanda ya nema a ranar 5 ga watan Augusta.

Sauraron shari’ar shugaban kungiyar Shi’a, (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zinat, zai cigaba a babbar kotun shari’a ta birnin Kaduna.

El-Zakzaky da matarsa suna hannun hukuma tun watan Disamban 2015, tun bayan rikicin da ya barke tsakanin kungiyar da sojojin Najeriya a Zaria.

Gwamnatin jihar Kaduna ta zargesu da laifuka 8, ciki har da zargin kashe mutane babu gaira ba dalili, taro ba bisa ka’ida ba da kuma tayar wa da mazauna yankin hankula, da sauran laifuka.

A ranar 29 ga watan Satumba, 2020, shugaban IMN da matarsa sun musanta zargin da ake yi musu, ta bakin lauyansu, Marshall Abubakar, wanda ya wakilci Femi Falana, shugaban lauyoyin.

Ya roki kotu da tayi fatali da kara da zargin da ake yi wa El-Zakzaky. Mai shari’a, Justice Gideon Kurada ya ki amincewa da wannan bukatar, bayan ya gama sauraron shari’ar.

Ya dage sauraron shari’ar zuwa 18 ga watan Nuwamba da ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2020.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here