Ina Farin Cikin Cika Alkawarin da na Yiwa Al’ummar Mutane Masu Nakasa – Shugaba Buhari
Buhari ya cika alkawarinsa ga al’ummar nakasassun Najeriya, a cewarsa.
Hajiya Sadiya Umar Farouq ta kai nakasassu fadar shugaban kasa.
Shugaba Muhammadu ya bayyana cewa lallai ya cika alkawarin da yayi wa al’ummar nakasassun Najeriya ta hanyar kafa musu sabuwar ma’aikata.
Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin hukumar nakasassun Najeriya.
Read Also:
Mambobin hukumar sun kaiwa shugaba Buhari ziyara ne ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu, 2021, karkashin jagorancin ministar walwala da jinkan jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq.
A jawabin da yayi a shafinsa na Tuwita @Mbuhari da yammacin Alhamis, Buhari ya bayyana cewa ya rattafa hannu kan dokar jin dadin nakasassu a Najeriya.
Hakazalika ya kaddamar da hukumar kula da nakasassu domin cigaba da aiki.
“Ina farin cikin cika alkawarin da na yiwa al’ummar mutane masu nakasa, ta hanyar rattaba hannu kan dokar nakasassu,” Buhari yace.
“Hakazalika mun rantsar da mambobin hukumar mutane masu nakasa domin cigaba da aikin da kuma wanzar da manufarmu.”