Mu ba Ci-ma-Zaune ba ne, Muna da Arziƙi – Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyarsa ta gyara Najeriya, yana mai bayyana ƴan ƙasar da cewa masu ƙwazo ne, saboda haka babu wani dalili da zai sanya su zauna cikin talauci.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar wasu dattawan ƙasar, da suka haɗar da jagororin jam’iyyun APC da PDP, a fadar shugaban ƙasa.
Read Also:
“Mu ba ci-ma-zaune ba ne, muna da arziƙi. Abin da muke buƙata shi ne taimakon junanmu, mu zama ‘yan uwa nagari. Ni ba shugaban ƙasar da zai ba da uzurririka,” kamar yadda mai magana da yawunsa ya bayyana.
“Zan yi aiki tuƙuru da manufofi masu kyau, da sadaukarwa da ƙwarin gwiwa don samar da arziƙi ga ƴan Najeriya,babu wani dalili da zai sanya mu zauna cikin talauci, ba za mu ci baya ba,”
Shugaban Tinubu ya ƙara da cewa “Ba wani abu ba ne, yanzu muna fuskantar tsanani, amma daɗin na gaba. Za mu cimma muradunmu tare da cika burukan kakanninmu. Ina samun ƙwarin gwiwa daga ƴan ƙasar da nake mulki.”
Tawagar shugabannin sun ce sun yi amanar cewa zai ciyar da Najeriya gaba, zai kuma cika alƙawurran da yayi wa ƴan ƙasar.