CNG: ‘Yan Arewa Karmu Dogara da Gwamnati da Sojoji
Wasu kungiyoyin arewa sun bukaci al’umman yankin a kan su tashi tsaye don ba kansu kariya a yayinda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa.
Kungiyoyin sun bayyana cewa daga yanzu al’umman yankin ba za su zauna suna jiran gwamnati da dakarun sojin kasar su karesu ba.
Read Also:
Hakan ya biyo bayan yankan rago da mayakan Boko Haram suka yi wa wasu manoma a garin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere, jihar Borno.
Gamayyar kungiyoyin arewa a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, sun jaddada kiransu ga al’umman garuruwan arewacin kasar a kan su tashi tsaye sannan su kare kansu.
Kungiyoyin sun yi kiran ne biyo bayan kisan kiyashin da aka yi wa manoma a garin Zabarmari, karamar hukumar Jere na jihar Borno.
Kakakin gamayyar, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce yanzu ba za a iya dogara a kan gwamnati da dakarun sojin kasar don ba garuruwan arewa kariya ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.