Kungiyar CNG ta Nuna Rashin Goyan Bayanta ga Gwamnonin Arewa Kan Haramta Kiwo a Fili
Gamayyar kungiyoyin arewa, CNG, ta nuna goyon bayanta ga neman afuwa da Sheikh Gumi ke son ganin an yi wa yan bindiga.
Kungiyar ta kuma soki gwamnonin arewa kan matakin haramta kiwo a fili ba tare da tanadin tsarin taimakawa makiyaya ba.
Har wa yau, kungiyar ta soki gwamnatin tarayya a kan abinda ta kira gazawarta wurin daukan matakan kawo karshen rikicin.
Gamayyar kungiyoyin arewa, CNG, ta goyi bayan Sheikh Ahmed Gumi na kira ga gwamnati ta yi wa yan bindigan da ke adabar jahohin arewa afuwa da nufin samun dawamammen zaman lafiya a yankin, Leadership ta ruwaito.
Read Also:
Kakakin CNG Abdul Azeez Suleiman cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Abuja, ya yi kira ga makiyaya Fulani da ke zaune a jahohin kudu su dawo idan har garuruwan da suke ba su maraba da su.
Ya ce, “Ba mu goyon bayan matakin da kungiyar gwamnonin arewa ta dauka na haramta kiwo a fili ba tare da kirkirar filayen kiwo ba bayan shafe shekaru hudu suna karyar za su bawa makiyayan matsuguni ta hanyar wasu shirye-shirye da har yau suka gaza yi.
“Muna ankarar da mutane kan yadda gwamnatin tarayya ta gaza daukan wani matakin na gaske don kawo karshen matsalar da hadin kan Nigeria.
“Muna goyon bayan Sheikh Ahmed Gumi a shirinsa na ganawa da yan bindiga da nufin ganin an musu afuwa, sauya tunani da cigaba da zama cikin mutane da wadanda suka rungumi zaman lafiya sannan a ragargaji wadanda ba su amince ba.
“Don haka, muna goyon bayan kokarin da gwamnatocin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi da wasu jahohi ke yi na sulhu a maimakon tsarin amfani da karfin bindiga da zubar da jini da irin na El-Rufai da masu ra’ayinsa,” in ji shi.