CNG: Shugabannin da ke Mulki a Kasar Nan Sun Gaza Kawo Gyera

Kungiyar CNG ta yi kaca-kaca da shugabannin da ke mulki a kasar nan.

CNG ta ce Gwamnonin jihohi da Gwamnatin Tarayya sun gaza kawo gyara.

Wannan shi ne ra’ayin wasu manyan Ibo da ke zaune a Arewacin Najeriya Gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) da wata kungiya ta shugabannin Ibo da ke Arewacin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu game da shugabannin kasar nan.

A taronsu, CNG da Igbo Community Leaders of Northern Nigeria sun yi ittifakin shugabannin Najeriya sun gagara hada kan al’umma da kawo cigaban kasa.

Vanguard ta ce kungiyoyin sun bayyana wannan ne a karshen zaman da su ka yi a Abuja, inda su ka fitar da jawabi cewa duka shugabanni masu-ci a yau, sun gaza.

Kungiyoyin ta bakin shugabannin da su ka yi magana a madadinsu, sun fitar da wannan matsaya ne ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasan shugabannin nan ba.

CNG da takwararta sun yi magana game da salon nadin mukaman gwamnatin tarayya ta Muhammadu Buhari da kuma kawo ayyukan da za su taimaki kasa.

Wadannan kungiyoyi sun fitar da jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun bakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, da sakataren kungiyar Ibon, Austin Ifedinezi.

Jawabin kungiyoyin ya yi kiran a rika tafiya da duka kabilun Najeriya wajen gudanar da mulki.

A wajen wannan taron har wa yau, kungiyoyin sun koka game da yadda sha’anin tsaro ya ke dada tabarbare wa, tare da bada shawarwarin da zai ceci al’ummar kasar.

A karshe, kungiyoyin Arewan sun yi Allah-wadai da yadda wasu su ka yi amfani da zanga-zangar lumanar #EndSARS wajen yin ta’adi a wasu bangarorin Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here