Wani Babban Tsohon Soja ya Shigar da Karar Buratai da Wasu Manyan Sojoji

Birgediya Janar Abubakar Sa’ad (mai ritaya) ya shigar da karar ilahirin rundunar soji a gaban kotun ma’aikata.

Tsohon sojan ya shigar da karar rundunar soji da jagorinta bayan an yi masa ritayar dole daga aiki.

Mohammed Adelogun, lauyan mai kara, ya ce kotu ta saka lokacin sauraron korafin da suka shigar, sai dai akwai tarnaki.

A ranar Talata ne birgediya janar (mai ritaya), Abubakar Sa’ad, ya shigar da karar ilahirin rundunar soji a gaban kotun ma’aikata (NIC) domin kalubalantar yi masa ritayar dole.

Sauran wadanda mai korafin ya ambata a cikin takardar shigar da kara sun hada da, babban hafsan rundar soji; Laftanal Janar Tukur Buratai, shugaban rundunar tsaro; Janar Abayomi Olanisekin, da kuma ministan tsaro; Bashir Salihi Magashi, da kuma majalisar koli da rundunar soji.

Lauyan mai kara, Mohammed Adelogun, ya ce kotu ta saka lokacin sauraron korafin da suka shigar.

A cewar lauyan, an fara shigar da karar ne a ranar 7 ga watan Satumba, 2016, amma sai kotu ta yi watsi da karar a ranar 16 ga watan Satumba, 2017, saboda rashin cika wata ka’ida.

Mista Adelogun ya ce kotu ta yi watsi da karar ne bayan wadanda ake kara sun yi korafin cewa mai kara ya sabawa tanadin dokar rundunar soji, kafin ya shigar da kara.

Lauyan ya kara da cewa mai kara ya kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara a cikin shekarar 2018, inda daga bisani kotun daukaka kara ta jingine hukuncin kotun farko.

Kotun daukaka kara ta bukaci a mayar da karar zuwa kotun NIC domin a saurari korafin birgediya janar Sa’ad, a cewar lauya Adelogun.

Kazalika, Lauyan ya bayyana cewa wadanda ake kara sun sake dakirewa, suna masu gardamar cewar tuni an gama da maganar, babu wani sauran zance, hasalima, sun ce; kotun ba ta da ikon sauraron korafin.

Ya bayyana cewa ya yi raddi ga martanin wadanda ake kara, sannan ya nemi izinin sauya wani bangare na korafinsu tare da bawa kotu hakuri a kan shigar da kara a kurarren lokaci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here