Abin Al’ajabi ‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Wasu Manyan ‘Yan Sanda

 

Lauya mai rajin kare hakkin bil’adama, Bulama Bukarti, ya yi tsokaci a kan rahoton da BBC Hausa ta wallafa.

A ranar Talata ne BBC Hausa ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun sace manyan jami’an ‘yan sanda har goma sha biyu a tsakanin jihar Katsina da Zamfara.

Labarin sace ‘yan sandan bai bayyana ba sai yanzu, bayan kwana goma, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

A cewar BBC Hausa, an sace ‘yan sandan ne kwanaki goma da suka gabata bayan ‘yan bindiga sun kai wa tawagarsu harin kwanton bauna.

Matar ɗaya daga cikin jami’an ƴansandan ita ce wadda ta shaidawa BBC cewa mijinta ya umarceta da ta siyar da gidan da suke zaune don samun kuɗin fansa.

Ta ce ta san iyalan sauran jami’ai takwas da aka sace su tare da mijinta.

Iyalan jami’an suna ta faman ƙoƙarin haɗa ₦800,000 kowannensu don biyan kuɗin fansa.

Lokacin da BBC ta tuntuɓi rundunar ƴansanda reshen jihar Borno, tunda daga nan ne aka tura jami’an, sai suka ce su tuntuɓi rundunar reshen jihar Zamfara ko Katsina.

Sai dai gaba ɗayansu wato rundunar jihar Borno, Zamfara da Katsina sun ce basu da wata masaniya dagane da lamarin.

Lauya mai rajin kare hakkin bil’adama, Bulama Bukarti, ya ce; “abun fargaba ne da razani yadda al-amura ke ƙara ta’azzara a yankin arewa maso yammacin ƙasar nan.

“Idan har za’a iya ƙwamushe jami’an ƴansanda cikin ayari, to me kuma ya rage, ina makomar sauran karabitin mutane dake zaune kara zube ba tare da makami ko horon kare kansu ba?

“Abune a bayyane, haƙiƙa muna wasa da wuta wadda nan gaba zata ƙona mu in har muka yi sake”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here