Wasu ‘Yan Bindiga Sanye da Kayan Sojoji Sunyi Garkuwa da Wasu Mutane

 

Yan bindiga sun mamaye shingen binciken hukumar haraji ta jihar Benue tare da yin garkuwa da ma’aikatan hukumar su biyar.

Har yanzu ba a san inda ma’aikatan suke ba duk kuwa da korafi da aka kai wa runudnar ‘yan sanda.

Har yanzu ba a ji ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar akan wannan al’amari ba Da yammacin Litinin ne yan bindiga suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan hukumar tara kudaden shiga ta jihar Benue a karamar hukumar Vandeikiya da ke jihar.

Da yake shaidawa manema labarai, mai magana da yawun shugaban hukumar, Ati Terkula, ya ce lamarin ya faru da misalin 6:30 na yamma kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Terkula ya ce, “yan bindigar sun kai hari shingen hukumar dake karamar hukumar Vandeikiya, suka lalata kayayyaki da kuma garkuwa da ma’aikata biyar da suke aiki a lokacin.

“Yan bindigar sun yi shiga cikin kayan sojoji cikin wata mota kirar Hilux da babura uku. Suka mamaye sansanin binciken hukumar a Vandeikiya, suka kona baburan ma’aikata, harbi kan mai uwa da wabi, kuma suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan hukumar tara kudaden shiga biyar da raunata wasu da dama.

“A halin yanzu, ba a san inda ma’aikatan suke ba, duk kuwa da cewa an kai korafi ga ofishin yan sanda na Vandeikiya.

“Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ya ci tura saboda an kasa samun wayar ta.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here