Jamhuriyar Congo da Rwanda Sun sa Hannu Kan Yarjejeniyar Dakatar da Yaƙi
Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da Rwanda sun cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi a gabashin Congo.
Read Also:
Ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu sun sa hannu kan yarjejeniyar bayan tattaunawar da shugaban Angola, Joao Lourenco ya shiga tsakani.
Yarjejeniyar za ta soma aiki ranar 4 ga watan Agusta mai kamawa lokacin da wa’adin yarjejeniyar jin ƙai tsakanin ƴan tawayen M23 da dakarun gwamnati ke cika.
Gwmanatin Congo ta zargi Rwanda da goyon bayan mayaƙan M23, da ke riƙe da wuraren da ke da albarkatun ƙasa.
Rwanda dai ta sha musanta waɗan nan zarge-zargen.