Zamu Saki Sojojin Rwanda Biyu da Aka Garkame a ƙasata – Shugaban Congo
Shugaban Angola Joao Lourenco, ya ce Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Congo ta amince su saki sojojin Rwanda biyu da ake tsare da su a makon da ya wuce, sakamakon tashin hankalin da ya faru a iyakar kasar.
Read Also:
Mista Lourenco, wanda ke shiga tsakani, ya yi wannan sanarwa ne bayan tattaunawa da takwarorinsa na Congo da Rwanda a lokuta mabanbanta.
Ofishinsa ya ce Felix Tshisekedi da Paul Kagame, sun amince da ganawar keke-da-keke a Angola, sai dai ba a tsaida rana ko lokaci ba.
Kasashen Rwanda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, sun zargi juna da daukar nauyin ‘yan ta’adda da ke kaddamar da munanan hare-hare a iyakokin ƙasashen biyu.