Abinda  Cutar Covid-19 ta Koya Min – Gwamnan Niger

 

Kebewata ta koyamin darasi, na tabbatar cutar COVID-19 gaskiya ce, cewar gwamnan jihar Niger.

Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, ya ce yayi amfani da killacewarsa wurin neman gafarar Allah.

Ya fadi hakan ne a ranar Talata, bayan ya dawo daga killacewar, har yayi taro da ‘yan majalisar jiharsa.

Gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello, ya ce yayi amfani da makonni 2 da aka kebesa a kan cutar COVID-19, wurin neman gafara wurin Ubangiji, Daily Trust tace.

Gwamna Bello ya sanar a shafinsa na Twitter, kwanaki 8 da suka gabata, cewa an auna sa, kuma an gane yana dauke da cutar COVID-19, kuma har ya riga ya killace kansa kamar yadda dokar cutar ta tanada.

Gwamnan ya kammala kwanakin killace kansa a ranar Talata, har ya kai ziyara majalisar jiharsa.

A cewarsa, “A cikin makonni 2 da na killace kaina na koyi darasi, domin na tabbatar da cewa cutar COVID-19 gaskiya ce. Ya kamata kowa ya kula kuma ya kiyaye dokokin kare kai daga cutar COVID-19.”

“Na yi amfani da makonni 2 da na killace kaina wurin neman gafarar mahalicci na. Ya kamata mu kula, kada mu shafawa iyalanmu cutar,” cewar gwamnan.

Bello ya yi a kalla sa’a daya tare da ‘yan majalisar jiharsa, a wani taron sirri, ya sanar da manema labarai cewa yayi godiya ga ‘yan majalisarsa, musamman wadanda suka nuna kauna da damuwa a garesa lokacin da yake killace.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here