CPC da Suka Narke a APC su na so Mataimakin Tinubu ya Fito Daga Tsaginsu
Akwai rabuwar kai tsakanin jagororin APC a kan wanda zai yi takarar mataimakin shugaban kasa.
Bangaren jam’iyyar CPC da suka narke a APC su na so mataimakin Bola Tinubu ya fito daga tsaginsu.
Yayin da ake kawo shawarar a dauki Kashim Shettima, akwai masu sha’awar Abubakar Malami.
Abuja – Lokaci ya karaso na zaben ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa, jam’iyyar APC ta na ta lissafin abokin takarar Bola Tinubu.
Wani rahoto da ya fito daga Daily Trust a ranar Talata, 14 ga watan Yuni 2022 ya nuna cewa kai ya rabu tsakanin ‘yan bangarorin da suka taru, aka kafa APC.
Wata majiya ta shaida cewa mutanen tsagin CPC da ke jam’iyyar APC mai mulki za su tunkari shugaba Muhammadu Buhari kan batun tikitin zaben 2023.
Wadannan manya su na shirin haduwa da shugaban kasa da nufin ba shi shawarar ya fadawa Tinubu wanda zai dauka a matsayin ‘dan takarar mataimaki.
Ana kawo mutane 2 a lissafi
Read Also:
Sunayen da wadannan mutane za su kai fadar shugaban kasan sun kunshi Ministocin gwamnatin tarayya; Abubakar Malami da Sanata Hadi Sirika.
Malami SAN shi ne yake rike da kujerar Ministan shari’a na kasa kuma babban lauyan gwamnatin tarayya tun 2015, yana da karfi a gwamnatin nan.
Shi kuma Hadi Sirika shi ne Ministan harkokin jiragen saman Najeriya. Kafin zamansa karamin Minista, ya taba yin ‘dan majalisar wakilai da Sanatan Katsina.
Amma ana tunanin cewa shugaban kasar zai yi watsi da shawarar mutanen na sa kamar yadda ya yi a wajen zaben ‘dan takaran APC, ya ki goyon bayan kowa.
Jaridar ta rahoto majiyar ta na cewa Buhari zai bar Bola Tinubu ne ya zabi wanda zai yi aiki da shi.
Matsayar Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ‘dan takarar shugaban kasar ya bar wuka da nama a hannun fadar shugaban kasa, a zaba masa duk wanda ya fi cancanta.
Majiyarmu wanda yana da kusanci da wani babban Gwamna a jam’iyyar APC ya shaida mana cewa fadar shugaban kasa ta na so ne Tinubu ya dauki Kirista.