FG: Za a Samu Hauhawar Wadanda Zasu Kamu da Cutar Korona a Karo na Biyu

Yawan masu korona a Najeriya zai karu sosai nan da makonni biyu masu zuwa.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba.

Mustapha ya ci gaba da bayyana cewa zabukan gwamnan Edo da Ondo, da kuma zanga-zangar EndSARS ne za su haddasa haka Gwamnatin tarayya ta tabbatar da tsoron kwararru a harkar lafiya da dama a fadin duniya game da dawowar annobar cutar korona a karo na biyu.

Boss Mustapha, babban sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin Shugaban kasa kan COVID-19 a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa za a fasinjoji da yawa za su shigo da cutar cikin kasar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mustapha ya daura laifin haka a kan wasu yan Najeriya da suka ki daukar gwaje-gwajen da ya kamata a yayinda suka iso kasar, inda ya bayyana cewa daga alkaluman mahukunta, mutum daya cikin uku ne ke gabatar da kansu don gwaji.

Babban sakataren gwamnatin ya kara da cewa zabukan Edo da Ondo, da kuma zanga-zangar EndSARS a fadin kasar, sun kara yawan cutar.

Ya ce: “PTF na ta jaddada wadannan lamura saboda muna cikin hatsarin shigowa da cutar, tunda an bude hanyar jiragen samanmu da kuma yawan yaduwar cutar sakamakon zanga-zanga. Makonni biyu masu zuwa za su zamo cike da hatsari.”

Mustapha ya bayyana cewa PTF ta yi barazanar daukar mataki a kan masu take doka sannan ta lura cewa da dama basa bayar da hadin kai.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here