ɓarkewar Cutar Kwalara: Mutane 146 Sun Rigamu Gidan Gaskiya
Cutar kwalara ta ɓarke a jahar Kebbi, inda aka tabbatar da ta kashe aƙalla mutum 146 a faɗin jahar.
Shugaban asibitin Sir Yahaya, Aminu Bunza, ya tabbatar da adadin a wata fira ta wayar tarho.
Gwamnatin jahar ta samar da kayan aiki da kuma magunguna domin yaki da cutar.
Kebbi – Akalla mutun 146 sun rasa rayukansu a jahar Kebbi, a cewar wani jami’in lafiya yayin da cutar kwalara da ta ɓarke a Najeriya ta shiga jahar.
Premium times ta ruwaito yadda cutar kwalara wacce take jawo amai da gudawa take kara cin karenta babu babbaka a Najeriya, inda abun yafi muni a yankin arewa maso yamma.
Cutar ta kashe mutun 75 a jahar Katsina zuwa ranar Talata, yayin da ta kashe 30 a Zamfara, 23 a Sokoto da kuma mutum 119 a Kano.
Kwalara ta shiga jahar Kebbi
Read Also:
A wata hira ta wayar tarho ranar Laraba da safe, Aminu Bunza, Sakataren Asibitin Sir Yahaya dake Kebbi, ya tabbatar da adadin da suka mutu a jahar.
Ya bayyana cewa an fara samun mai ɗauke da cutar kwalara a karamar hukumar Sakaba ta jahar.
Bunza yace akwai wasu mutum dubu 2,028 da suka kamu da cutar zuwa ranar Laraba.
Bunza yace:
“An fara samun mai ɗauke da cutar a kauyen Dirin Daji dake karamar hukumar Sakaba, inda zuwa yanzun ta shiga dukkan kananan hukumomi 20 na jahar.”
Wane mataki gwamnati ta ɗauka? Shugaban asibitin ya bayyana cewa gwamnatin jahar ta fara ɗaukar matakan da ya dace domin dakile yaɗuwar cutar.
Yace:
“Gwamnati ta samar da kayan aiki da magunguna a dukkan kananan hukumominta kuma ta baiwa ma’aikatan lafiya horo domin tabbatar da dakile yaɗuwar cutar har wurin da ba ta je ba.”
Bunza ya yi kira ga al’ummar jahar da su tabbatar da tsaftar gidajensu da kuma yankunan da suke rayuwa, sannan su sha ruwa mai tsafta kaɗai.