Zan Tashi Daga ‘Dan Najeriya Idan Tinubu ya Samu Mulki a 2023 – Bode George

 

Bode George ya yi wa Adeseye Ogunlewe raddi a kan tallar Bola Tinubu a 2023.

Jagoran na PDP ya ce zai tashi daga ‘Dan Najeriya idan Tinubu ya samu mulki.

George yayi wa masu goyon-bayan Tinubu kudin goro, yace ba a daidai suke ba.

Ogunlewe ya san Tinubu bai mallaki satifiket ba.

Legas – Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Bode George ya fito ya na cewa Bola Tinubu bai da wata takardar shaidar zuwa makaranta.

Jaridar The Cable ta rahoto Bode George yana maida martani ga Adeseye Ogunlewe wanda ke cewa Bola Tinubu ya kamata ya gaji Muhammadu Buhari.

‘Dan adawar ya ce ian aka tsaida Tinubu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa, bai da satifiket da zai gabatar da ke nuna ya yi firamare, sakandare da jami’a.

“Ogunlewe ya san ko Naira nawa aka ce za a bada, Tinubu ba zai iya kawo takardun makarantarsa ba (firamare, sakandare, da jami’a), domin ya san bai da su.”

Da ake hira da tsohon gwamnan a gidan talabijin, ya ce babu wani mai hankali da zai goyi bayan Tinubu, ya zargi tsohon gwamnan da satar kudin jahar Legas.

George yake cewa Tinubu ya na wawurar biliyoyi har yau daga asusun gwamnatin jahar Legas ta karkashin kamfaninsa na Alpha Beta da ke tattara haraji.

Me George zai yi idan hakan ta faru?

Har ta kai Premium Times ta rahoto George yana cewa zai tashi daga zama ‘dan Najeriya idan jagoran na jam’iyyar APC mai mulki, ya karbi mulkin kasar nan.

“Zan yi duk abin da zan iya in tashi daga zama ‘dan kasa idan hakan ta faru. Mutum irin wannan? Shin ka na tunanin jahar Legas za ta ga wani canji ne?

“A nan (Legas) muke zaune, dubi jahar. Babu hanyoyin ruwa, ka duba abin da suka yi a bakin teku.”

“In tsaya ina tunani a rain a cewa irin wannan mutum zai zama shugaban kasa…Ka je ka duba dukkaninsu (masu goyon bayan Tinubu), wani abu yana damunsu.”

Cif George ya zargi Ogunlewe da yin baki-biyu, yace idan aka binciko bayanan da ya yi a da, za a ji yana sukar Tinubu, sai ga shi yana tallarsa bayan ya dawo APC.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here