Kungiyar CYMSN ta Bayyana Wanda ta ke so ya Gaji Buhari a 2023
Wata kungiyar malaman Musulunci ta bayyana matsayarta kan wanda suke so ya zama shugaban kasa a zaben 2023.
Kungiyar ta bayyana cewa lallai Bayarabe Musulmi take so ya zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Kungiyar wacce ta yi zargin cewa an mayar da Yarabawa baya kan lamuran shugabancin kasar ta ce idan hakan bai samu ba lallai za ta nuna turjiya.
Abuja- Wata gamayyar kungiyar malaman musulunci Yarbawa a Najeriya (CYMSN) ta bayyana cewa lallai Bayarabe Musulmi ne zai zama shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa.
Kungiyar ta kuma koka kan yunkurin tauye hakkin Musulman kudu da kuma hana su damar yin takarar manyan mukamai na shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a kasar nan, jaridar Leadership ta rahoto.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, mukaddashin shugaban kungiyar, Sheikh AbduRasheed Mayaleke, ya bayyana cewa za su nuna turjiya a duk wani yunkuri na mayar da Musulman Yarbawa baya idan aka zo batun shugabancin kasa.
Mayaleke ya koka cewa irin wannan yunkurin bai dace da tsarin dimokradiyya ba kuma yana da illa.
Read Also:
Sai dai, ya yi gargadin cewa za a iya fuskantar gagarumin matsala idan jam’iyyun siyasa suka gabatar da dan takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa da ba Bayarabe Musulmi ba.
Jaridar Punch ta nakalto Meyaleke yana cewa:
“Kungiyar malaman musulunci Yarbawa a Najeriya sun nuna damuwa matuka game da abubuwan da ke faruwa dangane da zabar ‘yan takara da jam’iyyun siyasa ke yi gabanin babban zaben 2023 a Najeriya.
“Muna ta sanya idanu sosai kan tsari da shirye-shiryen jam’iyyun siyasa da kuma fatan nuna damuwarmu game da rikicin da zai kunno kai idan ba a kawar da shi ba.”
“Ba sabon labari bane cewa jam’iyyar adawa ta PDP ta zabi dan arewa a matsayin dan takarar shugaban kasarta duk da cewa ana tsammanin dan takarar zai fito daga kudu, bisa ga tsarin karba-karba da babban taron ya yarda da shi.
“A kan haka ne muke kira ga jam’iyyar All Progressives Congress da ta zabi dan kudu, kuma a wannan karon, musulmi, a matsayin dan takararta na shugaban kasa; bugu da kari akwai yarjejeniya mai tushe a farkon kafa jam’iyyar a 2014 kan haka.
“Kur’ani 17:34 yana cewa “…Kuma ku cika alkawari, domin za a tambaye ku game da alkawarin.”
“An dade ana mayar da kasar Yarbawa baya tsawon shekaru da dama idan ana magana kan shugabanci.A wannan karon, ba zai zama kasuwanci kamar yadda aka saba ba kuma idan jam’iyyar ta yi kuskuren hanamu damar samun shugaban kasa musulmi ta hanyar tsari mara fa’ida, ba za mu lamunta ba.”