Da Allah Muka Dogara – Muhammad Rili

 

RanarJumu’a dai dai da 16 ga watan Afirilu, 2021 ne mu ka mai da Fom ɗin neman sha’awar tsayawa takarar kujerar ƙaramar hukumar Ikara, zuwa ga babban ofishin jam’iyya ta jaha.

tare da rakiyar ɗimbin magoya baya daga mata da maza daga gundumomin ƙaramar hukumar Ikara 10 da mu ke da su, a ƙarshashin jagorancin shugaban tsare-tsare wato, mataimaki na musamman a fannin shari’a.

Wannan gagarumar nasara ta samu ne da taimako da jajircewar al’ummar da ke so da muradin ganin ci gaban Ikara da ƙoƙarin ganin an ƙwace ta daga faɗawa mugun rami.

Muna da kyakkyawan ƙuduri da tanadi na ganin mun rungumi kowa ba tare bambanci ba, da kuma bai wa ɓangaren mata kaso 40, maza kuma kaso 60 a cikin sha’anin mulki daga faɗin gundumomi 10 da mu ke da su a ƙaramar hukumar Ikara.

matuƙar Allah ya bamu dama, za mu yi ƙoƙarin ganin an bai wa mata da masu buƙata ta musamman ( disables) kyakkyawan kulawa matuƙa, ta hanyar jawo su a jiki da ba wasun su muƙamai da kuma koyawa sauran sana’o’in dogaro da kai.

Har yanzu dai tsarinmu da ƙudurorinmu ba su wuce na inganta ƙaramar hukumar Ikara ba wato samar da ( sabuwar ƙaramar hukumar Ikara) a tsawon lokaci ko wa’adin mulki, ta hanyar haɗa hannu da al’umar Ikara don aiwatar da kyakkyawan tsarin da zai amfanar da ƙaramar hukumar da al’ummarta.

Muna fata da addu’ar al’ummar Ikara za su yi amfani da damar da uwar jam’iyya ta jaha ta ba su na zaɓar shugabannin da za su shugabance su ( cards carry members) a shekaru uku masu zuwa.

da fatan za su yi amfani da wannan dama wajen zaɓen shuwagabannin da za su ɗaga darajar ƙaramar hukumar, su kuma kawar da waɗanda ba su dace da ci gaban ƙaramar hukumar ba.

Saboda haka, ina kira ga ɗaukacin al’ummar Ikara da su fito su ɓarje guminsu wajen zaɓen mutanen kirkin da za su wakilcesu a dukkan matakai.

Mu zaɓi canjin da muka daɗe muna nema, mu zaɓi canjin da za mu yi alfahari da shi a tsawon shekaru ma su zuwa.

Allah ya kawo wani yanayi da ya bai wa talaka damar ” zaɓi da kanka” to mu sani fa, irin mutanan da muka zaɓa a ranar 5 ga watan Mayu, da wanda za mu zaɓa a ranar 5 ga watan Juli 2021, to su ne za su jagoranci ɗaukacin al’ummar Ikara, don haka, ya kamata mu zaɓi shugabannin da ‘ya’yan da za a haifa a nan gaba za su yi mana addu’ar alheri saboda kyawun abin da muka zaɓa na nagartattun shuwagabanni.

Idan Muka yi Nasara, Ikara ta yi nasara !!!

Allah mu ke roƙo da ya ci gaba da bamu kariya, ya sa albarka a cikin gwagwarmayar ganin mun mai do da martabar ƙaramar hukumar Ikara daga hannun mutanen da suka gaza kawo sauyi.

Allah ya taimaki ƙaramar hukumar Ikara!
Allah ya taimaki jahar Kaduna!
Allah ya taimaki Najeriya!

Hon. Muhammadu Rili
#IkaraArise

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here