Sheikh Ɗahiru Bauchi ya Magantu da Harin Bam Kan Masu Maulidi a Kaduna
Sheikh Ɗahiru Bauchi ya buƙaci Bola Ahmed Tinubu ya tabbata an hukunta sojojin da suka kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna.
Fitaccen Malamin ya aike da saƙon ta’aziyya ga al’ummar Musulman Najeriya da na duniya kan wannan ibtila’i da ya ci rayuka.
Ya ce abin da ɗaure kai sojojin sama sun nesanta kansu da harin amma sojin kasa sun ce su suka yi kuskuren.
Jihar Bauchi – Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ya maida martani kan harin sojojin da ya halaka masu bikin Maulidi a Kaduna.
Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbata an hukunta duk mai hannu a kisan Musulmai a taron Maulidi a ƙauyen Tudun Biri.
Sama da mutum 90 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin bam ɗin sojijin kasa, wanda rundunar ta ce kuskure ne, ba da gangan ta yi ba, cewar Daily Trust.
Read Also:
Shahararren malamin ya kuma roƙi gwamnati ta gaggauta toshe duk wata kafa domin dakile yiwuwar tashin rikici da tsare rayuka da mutuncin yan Najeriya.
Shehin malamin ya aike da saƙon ta’aziyya
Ɗahiru Bauchi ya kuma jajantawa iyalan mamatan da daukacin al’ummar musulmi, kana ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu, ya kuma saka musu da gidan Aljanna.
Ya ce shi da mabiyansa suna cikin bakin ciki kuma sun kasa fahimtar dalilin da ya sa wasu ke kashe musulmai da ba su da hannu a tayar da hargitsi ko rashin zaman lafiya.
Shehin Malamin ya ce:
“Muna son gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta shiga tsakani, ta tabbatar da adalci ga wadanda suka rasa rayukansu a harin Mauludi, kuma a hukunta sojojin da suka aikta laifin.”
“Muna cikin yanayin ruɗani, su kuma shugabanni sun rufe idonsu kan waɗanda ake zalunta, waye mai lafi? Gwamnati ko wani daban? Bai kamata a yi wasa da koken mutane ba.”
“Muna jaddada bukatar mahukunta su gudanar da cikakken bincike kan wannan bala’i da ya yi ajalin mutane da yawa. A binciko yadda aka yi jirgin ya saki bam a taron Maulidi, sojojin sama sun ce ba ruwansu, na ƙasa sun ce su suka yi.”