Rundunar ‘Yan Sanda Jihar Borno ta daƙile Mummunan Shirin Dasa Bam a Jami’ar UNIMAID

 

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta samu nasarar daƙile wani mummunan shirin salwantar da rayukan jama’a a jami’ar UNIMAID.

Rundunar ta ce ta samu nasarar kwance wani bam da aka dasa a ƙofar shiga jami’ar a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce ba a samu asarar rai ko ta dukiya ba.

Jihar Borno – Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce ta samu nasarar kwance wani bam da aka dasa ƙofar shiga jami’ar Maiduguri a ranar Litinin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a Maiduguri, cewar rahoton Leadership.

Daso ya ce da misalin ƙarfe 9:00 na safe, a ranar Litinin 4 ga watan Disamba, an gano wata na’urar da ake zargi a kusa da babbar ƙofar makarantar.

Ya ce, rundunar ta gaggauta tura tawagar ƴan sandan da ke kula da ababen fashewa (EOD) zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tabbatar da cewa na’urar bam ce.

“Cikin gaggawa tawagar ta EOD ta fara aiki inda cikin nasara ta kwance bam ɗin ba tare da asarar rai ko dukiya ba.”

Daso ya ce rundunar ta kuma tsaftace yankin domin tabbatar da tsaro.

Wane ƙoƙari rundunar ƴan sandan ke yi?

Ya ce rundunar ta fara bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika da kuma dalilinsu.

Kakakin ƴan sandan ya bukaci mazauna jihar da su kai rahoton duk wani abu ko wani mutumin da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro mafi kusa da su domin daƙile asarar rayuka da dukiyoyi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com