Mutane 12 Sun Mutu, 30 Sun Jikkata a Hatsarin Mota a Jihar Plateau

Ana cikin jimami yayin da mutane 12 su ka gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Plateau.

Akalla mutane 30 ne su ka jikkata a hatsarin wanda ya rutsa da su a Hawan-Kibo da ke karamar hukumar Riyom a jihar.

Kwamandan hukumar FRSC, Godwin Alphonsus ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a birnin Jos.

Jihar Plateau – Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane 12 da jikkata wasu fiye da 30 a jihar Plateau.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a yankin Hawan-Kibo da ke karamar hukumar Riyom a jihar.

Yaushe hatsarin ya faru a Plateau?

Punch ta tababar cewa motar tirela ce makare da hatsi da kuma mutane ta kife yayin da ta ke haurawa a hanyar lokacin da abin ya afku.

Wani shaidar gani da ido ya ce bayan motar ta kife dukkan hatsin ya zube a ramuka tare da barin mutane matattu nan take, cewar Daily Post.

Kwamandan hukumar FRSC a jihar, Mista Godwin Alphonsus ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba a Jos.

Wane martani hukumar FRSC ta yi?

Ya ce:

“Hatsarin ya afku ne da tsakar rana a jiya Alhamis inda tirelar ta kife a cikin rami yayin da take haura hawan titin. “Motar na dauke da hatsi da kuma mutane yayin direban ya rasa birki lokacin da ya ke haura hawan.

“Tun a lokacin, mutanen mu da ke Hawan-Kibo su ka isa wurin inda aka tabbatar mutane 11 sun mutu.”

Alphonsus ya ce take su ka dauki mutane fiye da 30 da su ka jikkata zuwa asibiti mafi kusa don ba su kulawa na musamman, cewar Platinum Times.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com