LGBT: Jaridar Daily Trust ta Bayar da Haƙuri Kan Labarin Yarjejeniyar SAMOA

 

 

Jaridar Daily Trust ta bayar da haƙuri kan labarin da ta yi na yarjejeniyar Samoa, wanda ya tayar da ƙura.

A wata sanarwa da ta fitar, mai taken, Yarjejeniyar Samoa: Muna bayar da haƙuri, ta ce, “A jaridarmu ta 4 ga Yulin 2024, babban labarinmu mai taken, “LGBT: Najeriya ta shiga yarjejeniyar biliyan $150 da Samoa”, labarin ya tayar da ƙura a faɗin ƙasar. Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara a gaban hukumar sauraron ƙararrakin da suke da alaƙa da jaridu wato National Media Complaints Commission (NMCC), wanda aka fi sani da Ombudsman.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “bayan sauraron kowane ɓangare, NMCC ta gano cewa akwai kura-kurai a labarin, sannan an kauce daga wasu ƙa’idojin aikin jarida waɗanda ya kamata kowace jarida ta kiyaye.

Mun amince da wannan matsaya ta NMCC. Muna ba gwamnatin tarayya haƙuri, sannan muna ba masu karanta jaridunmu da dukkan sauran mutane haƙuri bisa kuskuren da muka yi.”

Dangane kuma da hanyoyin da jaridar ke bi wajen tantance labaranta, jaridar ta ce “hanyoyin da muke bi wajen tantance labari suna da inganci, kuma sun taimaka mana wajen gudanar da ayyukanmu na sama da shekara 25. Amma duk da haka, bayan wannan kuskuren, mun sake dubawa tare da inganta su.

“A matsayinmu na gidan jarida, burinmu shi ne samar da labarai masu inganci da samar da haɗin kan ƙasa da tsaronta da kuma tabbatar da cigabanta. Muna yin hakan ne ta hanyar fitar da labarai da za su taimaka wa mutane wajen fahimtar duniya da kuma bayar da damar tafka muhawara da kuma bin diddigin harkokin shugabanci.

Daga ƙarshe jaridar ta sanar da cewa ba ta yi labarin ba da nufin nuna hamayya ga wata gwamnati “ba ma goyon baya, ko kuma adawa da kowace gwamnati ko jam’iyya, ko ɗaiɗaikun mutum. Burinmu shi ne samar da gaskiya domin ilimantar da mutane.Amma kamar sauran jaridu, dole wasu lokutan za mu iya yin kuskure,” kamar yadda Daily Trust ta ƙara haske.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here