Lokaci ya yi da Gwamnatin Najeriya za ta Daina Biyan Tallafin Man Fetur – Dangote
Shugaban matatar man fetur ta Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta daina biyan kuɗin tallafin man fetur.
Dangote ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da Blomberg a ranar Litinin, inda ya ce biyan tallafin na sa gwamnatin “kashe kuɗaɗen da bai kamata ba,” wanda hakan ya sa akwai buƙatar a dakatar da shi, sannan ya ƙara da cewa ita kanta gwamnatin Najeriya ba za ta iya cigaba da biyan kuɗin tallafin ba.
“Ina tunanin lokaci ya yi da za a daina biyan kuɗin tallafin nan domin dukkan ƙasashe sun daina biya.
Read Also:
“Farashin man fetur ɗinmu kusan kashi 60 ne farashin ƙasashen da muke maƙwabtaka da su, kuma iyakokinmu babu cikakken tsaro. Don haka ba za a iya cigaba da kashe irin kuɗaɗen nan ba,” kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da Bloomberg.
Dangote ya ƙara da cewa man fetur ɗin da matatarsa ke fitarwa zai taimaka wajen rage wa Naira nauyi.
Ya ce, “Batun tallafin fetur magana ce babba. Idan ka bayar da tallafi a kan wani abu, wasu sai su riƙa ƙara yawan abun domin su samu ƙarin kuɗaɗe sannan sai nauyin ya ƙare a kan gwamnati. Zai fi dacewa a daina biya baki ɗaya.
“Matatarmu za ta magance matsaloli da dama. Za ta bayyana asalin adadin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya saboda babu wanda zai iya faɗa maka a yanzu adadin litar man fetur da ake amfani da shi. Wasu za su ce maka lita miliyan 60 a kullum, wasu suna cewa bai kai ba. Amma mu yanzu za mu iya kididdigewa. Sannan za mu saka na’urorin bibiyar motocinmu domin tabbatar da cewa a Najeriya suke sauke man.”