Ku Daina Tsine wa Shugabanni duk Yadda Abubuwa Suka Lalace – Sarkin Musulmai
Mai alfarma Sarkin Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga ƴan Najeriya da cewa da su riƙa yi wa shugabannin ƙasar addu’a duk yanayin da ake ciki, kuma duk yanayin da ƙasar ke ciki.
Read Also:
Sultan ya yi wannan kiran ne a Jami’ar Ilorin a ranar Alhamis a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron ƙaddamar da littafin da aka rubuta a kan shugaban hukumar JAMB Farfesa Is’haq Oloyede, wanda ya yi ritaya daga aikin jami’a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sultan ɗin ya ƙara cewa, “ku daina tsine wa shugabanni duk yadda abubuwa suka lalace, maimakon haka gara ku riƙa musu addu’a. Ku daina faɗin abubuwa marasa kyau a kansu. Duk lalacewar shugaba ku guji tsine masa,” in ji shi.
A nasa jawabin, ministan shari’a Lateef Fagbemi (SAN), wanda shi ne shugaban taron, kira ya yi ga ƴan Najeriya da su riƙa ƙarfafa wa shugabanninsu gwiwa.
“Ban ce babu matsala ba, amma da zarar kun fara ɓata ƙasarku a idon duniya, ban san me muke tuna wa duniya ba game da ƙasar.