Dakarun Hukumar Tsaron Najeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga 42 a Yankin Shiroro Dake Jahar Neja
Dakarun Najeriya da suka hadar da sojoji da kuma ‘yan sanda sun kashe wasu ‘yan bindiga a kauyen Alawa da ke yankin Shiroro a Jahar Neja.
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa dakarun hadin gwiwar sun yi wa ‘yan bindigar kwantan bauna ne, wadanda ke kokarin tserewa aikin da sojojin Najeriya ke yi a jahar Zamfara.
Read Also:
Wata majiya ta kuma shaida wa jaridar cewa yayin wannan dauki ba dadi an kashe soja guda da kuma wasu da suka ji raunuka.”Dakarun sun samu rahoton sirri na fitowar ‘yan bindigar daga Zamfara sun nufin kauyen Alawa.
“Sun tsallake wasu wurare da sojoji suke bincike a cikin dazuka, amma mun samu damar far musu a Manganda. a kalla an kashe mutum 42 daga cikin su da yawa sun tsere da ciwuka a jikinsu.
“An kashe mana soja daya, an kuma dauki sauran mutanenmu da suka jikkata zuwa Asibitin Asma’u da ke Kagara.
“Mun kwace wasu makamai da babura da dai wasu abubuwa masu yawa, in ji wannan majiyar tasu.