Hadin Baki da ‘Yan Bindiga: Sarkin Katsina ya Dakatad da Hakimin Kankara, Abubakar Yusuf

 

Ana zargin wani Sarkin gargajiya da goyawa yan bindiga baya a garin Katsina .

Wannan ya biyo bayan mutuwan dan bindigan da ya sace dalibai a Kankara.

An dakatad da Hakimin har sai bayan an kammala bincike a kansa .

Masarautar Katsina ta dakatad da da Hakimin Garin Kankara, Abubakar Yusuf, kan zargin hada baki da yan bindiga da suka addabi al’ummarsa.

Kakakin majalisar Sarki, Iro Bindawa, a ranar Asabar ya bayyana cewa an dakatad da Hakimin ne bisa korafe-korafen mazauna gari da kuma binciken jami’an tsaro.

Kakakin ya kara da cewa an dakatad da shi ne domin taimakawa gwamnati wajen kawo karshen ayyukan yan bindiga.

Majalisar ta kaddamar da kwamiti don binciken Hakimin bisa zarge-zargen da ake masa na taimakawa yan bindigan da suka addabi jama’arsa.

Ire-iren haka suna faru a jahar Katsina inda akayi zargin Sarakunan gargajiya da hada kai da yan bindiga wajen cutar da al’ummarsu.

A kwanakin baya, gwamnan jahar Zamfara ya kwancewa Sarkin Maru rawani.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here