Abinda Yake Kokarin Dakatar da Cigaban Arewacin Najeriya – ACF
ACF ta ce ta’addanci yana kokarin dakatar da cigaban arewacin Najeriya.
Cikin ‘yan watannin nan ‘yan bindiga suna ta kai hari wuri-wuri a arewa.
Sun bayyana hakan ne a wata takarda ta ranar Alhamis a Kaduna ACF ta ce ta’addanci ne abinda yake mayar da arewa baya.
Dama an jima ana kai hari yankin arewa a cikin watannin da suka gabata, jaridar The Cable ta ruwaito.
A wata takarda wacce suka gabatar a ranar Alhamis karshen wani taro da suka yi a Kaduna, inda kungiyar tace ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane ne suke mayar da arewa baya. Audu Ogbe , tsohon ministan noma ne ya jagoranci taron.
Read Also:
“Dangane da rashin tsaro, kungiyar ta bayyana takaicinta ta yadda harkokin arewa da kuma na Najeriya gaba daya,” kamar yadda kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe ya karanta.
“Kungiyar nan ta yi Allah wadai da ayyukan da ‘yan ta’adda suke yi a arewa, inda yace kashe-kashensu ya yawaita duk da dan yankin ne yake shugabancin kasa.
“Kungiyar ta koka a kan yadda wasu suka jagoranci rura wutar tashin hankali ta bangaranci da addini a cikin wannan tashin hankalin da ake ciki.”
Sannan sun tattauna akan yadda har yanzu wasu dalibai suke hannun masu garkuwa da mutane ba tare da gwamnati ta yi wani ba.
Sannan sun nuna takaicinsu kwarai akan yadda ake ware dukiyoyi ana biyan masu garkuwa da mutane wanda ko a musulunci basa aiwatar da ayyuka nagari.
Kuma zasu yi amfani da dukiyoyin don cutar da al’umma.