Mata 7 da Suka fi Arziki a Duniya a 2021
Mata na kara nuna bajintarsu a duniya inda a wasu wuraren suke gogaya da maza wurin wasu ayyuka da sana’o’i da a baya ba haka lamarin ya ke ba.
Bakwai daga cikin wadannan matan sune suka fi sauran arziki a duniya.
Kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana, wadanan sune mata bakwai da suka fi arziki a duniya.
1. Francoise Bettencourt Meyers da Iyalanta
Francoise Bettencourt Meyers itace mafi mafi arziki a duniya, an kiyasta arzikinta ya kai $73.6 biliyan (29,089,375,000,000).
Ta gaji arzikin ne daga mahaifiyarta, Liliane Bettencourt wacce ta rasu a 2017.
Mahaifin Liliane ne ya kafa kamfanin kayan shafe-shafe na L’Oreal, inda Francoise ta yi aiki a nan tun 1997. A yanzu shekarunta 67.
2. Alice Walton
Dukiyar Alice Walton, yar Amurka, mai shekaru 71, ya kai $61.8 biliyan (N23,561,250,000,000) hakan yasa itace mace ta biyu mafi dukiya a duniya.
Ta samu dukiyarta ne daga manyan kantina na Walmart.
3. MacKenzie Scott
Read Also:
Dukiyar tsohuwar matar Jeff Bezo’s ya kai $53 biliyan (N20,206,250,000,000).
Ta samu dukiyarta ne daga kamfanin Amazon. Aurenta da Bezos ya zo karshe a 2019, wadda hakan yasa ta shiga jerin biloniyoyi a duniya.
Shekarunta 53 kuma yar kasar Amurka ne.
4. Julia Koch da Iyalanta
Dukiyar Julia Koch ya kai $46.4 biliyan (17,690,000,000,000).
Ita da ‘ya’yanta sun mallaki kashi 40 cikin 100 na kamfanin Koch industries.
5. Miriam Adelson
Miriam Adelson ce mace ta biyar mafi dukiya a duniya, dukiyarta ya kai $38.2 biliyan (N14,563,750,000,000). Shekarunta 75 a duniya, ita ce ta mallaki kashi 56 cikin 100 na gidan wasanni na Cas*no a Las Vegas.
6. Jacqueline Mars
Jacqueline Mars ta mallaki $31.3 biliyan (N11,933,125,000,000).
Ta samu dukiyarta ne daga kamfanin Mars Incorporated, kamfani mai yin alawa da abinci da abincin dabobi. Shekarunta 81 kuma yar kasar Amurka ce.
7. Yang Huiyan da iyalanta
Yang Huiyan, yar kasar China mai shekaru 39 itace ke da kashi 58 cikin 100 na kamfanin dillancin gidaje na Country Garden Holdings.
Dukiyarta ya kai $29.6 biliyan (N11,285,000,000,000).