NDLEA ta Kama Masu Safarar Miyagun ƙwayoyi a Legas
Read Also:
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA a Legas sun kama wasu da ake zargi da tarin ganyen wiwi da tramadol da sauran miyagun ƙwayoyi na biliyoyin naira.
Jami’an hukumar sun kai samame a wurrare daban-daban ciki har da tashoshin ruwa da jiragen sama da wani wurin ibada.
Wannan ba shi ba ne karon farko da NDLEA ɗin take kamawa tare da gabatar da waɗanda aka kama bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.