Akwai Yiyuwar Raguwar Farashin Kudin Man Fetur

 

Darajar man fetur ya na kara yin kasa a kasuwannin Duniya a yanzu.

Hakan ya na nufin kudin da ake saida fetur a gidajen mai zai yi kasa.

Kungiyoyin IPMAN da PPROON su na hararo raguwar farashin man Rahotanni daga jaridar Punch ta rahoto cewa man da Najeriya ta ke saida wa a kasuwar Duniya ya na cigaba da rage daraja a halin yanzu.

A ranar Alhamis, 8 ga watan Afrilu, 2021, farashin gangar man ‘Brent’ ya sake yin kasa a kasuwa.

Rahotanni daga kasar waje sun tabbatar da cewa gangar man Brent ya tashi ne a kan fam $62.92 da kimanin karfe 6:00 na yammacin jiya Alhamis.

Idan aka kamanta farashin da abin da aka saida man na Najeriya a tsakiyar makon nan, kowace ganga ta rasa $0.24, kusan N100 a kudinmu na gida.

Masana da ‘yan kasuwa su na ganin cewa idan aka cigaba da tafiya a haka, za a kai lokacin da dole farashin man fetur ya ragu a gidajen man Najeriya.

Masu kasuwancin mai a Najeriya sun shaida wa jaridar Punch cewa farashin zai fi tasiri idan gwamnatin tarayya ta zare hannunta daga harkar.

Tun a watan jiya da farashin gangar mai ya doshi $70, har yanzu bai sake tashi ba. A kullu-yaumin farashin man fetur fadu wa kasa yake yi a kasuwa.

A watan Maris ne gangar mai ya yi tashin da bai taba yi ba a cikin sama da shekara guda. Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, ganga ta tashi a kan N24, 000.

Babban jami’in kungiyar IPMAN, Cif Chinedu Ukadike, ya tabbatar da cewa watakila farashin fetur ya sauka a gidajen mai idan gangar mai ya tsaya a haka.

Wannan shi ne ra’ayin shugaban kungiyar Petroleum Products Retail Outlets Owners, Mista Billy Gillis-Harry, ya na mai ba gwamnati shawara ta cire hannunta.

Kwanaki kun ji cewa gwamnatin tarayya na shirin kara farashin dakon man fetur.

Rahotanni sun bayyana cewa za a rage kudin kowane lita daga N7.51 zuwa N9.11 Sakataren hukumar da ke tsaida farashin man fetur na kasa, Alhaji Ahmed Bobboi, ya bada wannan sanarwar bayan wani taro da aka yi da masu motocin haya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here