Dakatar da Fubara ya Saɓawa Tsarin Mulki – NBA
Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA ta ce sanya dokar ta-ɓaci a jihar Rivers da kuma dakatar da gwamnan Jihar Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar na watanni shida, ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Read Also:
Shugaban ƙungiyar, Mazi Afam Osigwe SAN, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu ya ce ayyana dokar da shugaba Tinubu ya yi sakamakon rikicin siyasa a jihar zai yi wa dimokraɗiyya da tsarin mulin ƙasar illa mai yawa musamman ga sashe na 305 na kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 wanda ya bayyana matakan ayyana dokar wanda kuma shugaban ƙasar ke iƙirarin ya dogara da su.
Sanarwar ta kuma ce tsarin mulkin ƙasar na 1999 bai bai wa shugaban ƙasa ƙarfin cire zaɓaɓɓen gwamna ko ƴan majalisu ba ta hanyar fakewa da dokar ta-ɓaci, sai dai tsarin mulkin ya zayyana matakan cire gwamna da mataimakin gwamna a ƙarƙashin sashe na 188.
Hakazalika, ƙungiyar ta ce cire ƴan majalisar dokoki da kuma rushe majalisa na ƙarƙashin tanadin tsarin mulki da dokokin zaɓe, waɗanda alamu ke nuna babu wanda aka bi cikinsu kafin ɗaukar wannan matakin.
Ƙungiyar ta NBA ta kuma jaddada cewa yanayin da ake ciki a Rivers na zazzafar rikicin siyasa, bai cika sharuɗɗan tsarin mulkin ƙasa na cire zaɓaɓɓun shugabanni ba.