An Dakatar da Magoyin Bayan Crystal Palace, Robert Garland
An dakatar da wani mai goyon bayan Crystal Palace daga duk wani abin da ya shafi kwallon kafa na tsawon shekara uku saboda kalaman wariyar launin fata da ya furta kan dan wasan Tottenham da Koriya ta Kudu Son Heung-min.
Robert Garland ya amsa laifin cin zarafi na wariyar launin fata a cikin watan Agusta bayan ya yi ihu da nuna alama ga Son a Selhurst Park a watan Mayu.
Da farko an yanke masa hukuncin sa’o’i 60 na aikin sa kai da kuma tarar fam 1,384.
Read Also:
Spurs da ‘yan sandan Birtaniyya sun ɗaukaka ƙara zuwa sashen masu kula da kwallon kafa na Birtaniya kan hukuncin.
Sanarwar da Tottenham ta fitar ranar Laraba ta ce ‘yan sandan Metropolitan sun goyi bayan kulob din, kuma sun tunkari sashen ‘yan sanda masu kula da kwallon ƙafa na Birtaniya don neman ɗaukaka ƙara game da hukuncin da aka yanke, kuma sakamakon haka kotu ta ba da umarnin dakatar da wanda ake tuhuma na tsawon shekaru uku,”
Garland, mai shekaru 44, ya nuna wariyar launin fatar ne bayan da aka sauya Son a minti na 89 a wasan da Tottenham ta doke Crystal Palace da ci 1-0 a ranar 6 ga Mayu 2023.