Duk da an Dakatar da Ibrahim Magu,Yana Karkashin Tsarin Albashin Gwamnatin Tarayya – Muhammad Dingyadi

 

Ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, ya fallasa bayanan halin da ake ciki game da lamarin Ibrahim Magu.

Ministan ya bayyana cewa tsohon mukaddashin shugaban EFCC ɗin yana nan a tsarin ma’aikatan gwamnatin tarayya dake ɗibar albashi.

Yace a halin yanzun an mika rahoton binciken kwamiti ga shugaban ƙasa, ana jiran ɗaukar mataki na karshe.

Abuja – Ministan harkokin rundunar yan sanda, Muhammad Dingyadi, yace Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban EFCC, ya na cikin tsarin albashi na FG, kamar yadda the cable ta rawaito.

Ministan ya yi wannan furuci ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta Channels tv, ranar Talata.

Da yake magana kan lamarin Magu, Ministan ya bayyana cewa tun bayan mika rahoton bincike ga shugaban ƙasa, ba’a sake tuntuɓar ma’aikatar ba ko hukumar yan sanda.

Minista Dingyadi yace:

“Abinda na sani shine an mika sakamakon bincike ga shugaban ƙasa, kuma har zuwa yanzun ba’a tuntubi ma’aikatar yan sanda ko hukumar yan sanda ba game da lamarin.”

“A halin yanzun muna jiran mu ji abinda sakamako na ƙarshe zai fito, a bayyana wa kowa yasani.”

Shin har yanzun Ibrahim Magu ma’aikacin gwamnati ne?

Ministan yace duk da an dakatar da Ibrahim Magu, daga muƙamin mukaddashin shugaban EFCC, har yanzun shi jami’in rundunar yan sanda ne kuma yana karkashin tsarin albashi na gwamnatin tarayya, Punch ta rawaito.

“Kamar yadda kuka sani an gudanar da bincike, kuma mutumin yana nan kan aikinsa, yana nan a hedkwatar yan sanda. Bana son yin magana sosai a wannan lokacin game da abinda ya faru da rahoton kwamiti.”

“Har yanzun shi ɗan sanda ne, duk da an dakatar da shi. Amma abinda kowa ya sani ya rike mukamin mukaddashin EFCC, yanzun kuma ya bar wurin.”

“Hakan ba yana nufin ya fita tsarin albashin FG bane, shi ma’aikaci ne, jami’in ɗan sanda ne daga nan har zuwa sanda aka ɗauki mataki na karshe kan lamarin.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here