Mohammed Gharouda ya Bukaci Hukumar Zaɓen Kasar Libya da ta Dakatar da Takarar Saif al-Islam Gaddafi

 

Babban mai shigar da kara na sojin Libya, Mohammed Gharouda, ya bukaci hukumar zaben kasar ta dakatar da takardun neman takarar Saif al-Islam Gaddafi, dan marigayi shugaban kasar Muammar Gaddafida ke neman takarar shugaban ƙasa.

Mai gabatar da kara ya kuma bukaci a dakatar da takardun takarar Khalifa Haftar – wanda shi ma ke neman shugabancin Libya.

Hukumar zaɓe a ranar Lahadi ta ce Saif al-Islam Gaddafi ya gabatar da takardun takararsa a zaɓen da ake shirin gudanarwa a wata mai zuwa.

Amma a cikin wata wasiƙa da ya aikewa hukumar zaɓe, Mr Gharouda ya yi gargaɗin cewa hukumar za ta yi kuka da kanta ga abin da zai biyo baya idan har ba ta dakatar da aikin takardun ba

“Ana zargin Saif al-Islam da Khalifa Haftar da aikata laifuka” kuma dole a dakatar da buƙatar takararsu har sai an kammala bincike,” kamar yadda babban mai gabatar da ƙarar ya bayyana a cikin takardar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here