Jami’an Sojoji Sun Dakile Rikici Tsakanin ‘Yan Asalin Yankin Jos da Hausawa a Jahar Filato

 

Jami’an sojoji sun yi nasarar dakile wani mummunan rikici da ka iya kazanta a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jahar Filato.

Rikicin dai ya barke ne a tsakanin ‘yan asalin yankin da Hausawan da suka yi kaka-gida.

Lamarin wanda ya afku a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, ya yi sanadiyar jikkata wasu mutane 10.

Jos, Filato – Matakin gaggawa da jami’an tsaro suka dauka a ranar Litinin ya dakile wani lamari da ka iya zama kazamin karo tsakanin ‘yan asalin yankin da Hausawa mazauna karamar hukumar Jos ta Arewa a jahar Filato.

An shiga halin fargaba a jahar bayan hare-haren da makiyaya suka kaddamar a kananan hukumomin Bassa da Riyom, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama da kone-konen gine-gine.

Makiyayan sun kuma lalata manyan gonaki na ‘yan asalin yankin.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa matakin gaggawa da jami’an Operation Safe Haven (OPSH) suka dauka ya hana rikicin ya rikide zuwa na zub da jini.

Wata majiya da ke kusa da wurin da abin ya faru a Naraguta ta bayyana cewa Hausawa da sanyin safiyar Litinin sun gano wata hanya da karkatar da ita zuwa inda ake binne Musulmi a Yelwa Zangam a cikin garin.

Saboda haka sai suka yi kokarin hana wadanda ke tona hanyar ruwar da ke kusa da makabartar.

An tattaro cewa an samu gagarumin saɓani, wanda ya ja hankalin sauran mutane a cikin garin, wanda ya haifar da tashin hankali inda mutane goma suka sami raunuka daban-daban.

An kuma tattaro cewa jami’an OPSH, waɗanda suka isa lokacin sun takaita lamarin daga tabarbarewa.

Kansilan gundumar, Hon. Yusuf Ali, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi zargin cewa ‘yan asalin yankin na kokarin karkatar da wata hanya kusa da wurin binne Musulmai zuwa wani wuri mafi aminci sai Hausawa suke ganin hakan a matsayin wata dabara ce ta kutsawa cikin makabartar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Filato ASP Gabriel Ubah ya shaida wa jaridar The Nation cewa:

“Ina sane da lamarin amma har yanzu ban samu cikakken bayani ba. Da zaran na samu, ba zan jinkirta ba ku ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here