Dalar Amurka ta yi Mummunar Faɗuwa Saboda Harajin Amurka
Darajar dalar Amurka ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba cikin shekara uku a kan kuɗin euro a ranar Juma’a, sakamakon ƙarin harajin da ƙasar ta sanya kan kayayyakin wasu ƙasashe a makon jiya.
Read Also:
To sai dai Shugaban Ƙasar, Donald Trump ya ce a kowane lokaci dalar za ta ci gaba da zama kuɗi mai farin jini a duniya.
Haka kuma masana sun nuna damuwa kan yadda ake sayar da kuɗin lamuni na Amurka.
Tun da farko, Fadar White House ta dage cewa harajin da Amurka ke ƙaƙaba kan kayayyakin da ake shigar da su ƙasarta zai azurta ta.
Wata babbar jami’a a babban bankin Amurka, Susan Collins ta ce bankin a shirye yake ya samar da daidaito a kasuwanni idan buƙatar hakan ta taso.