Dalibar Aji 1 a Sakandire ta Kai Karar Gwamnatin Jahar Ekiti Gaban Kotu

 

Gift Agenoisa, wata dalibar JSS1 a makarantar sakandaren Mary Immaculate dake Ado-Ekiti, ta maka gwamnatin jahar Ekiti a babbar kotun jahar.

Gift tana bukatar gwamnati ta biya ta naira miliyan 15 sakamakon shiga hakkinta da gwamnatin tayi na dakatar da karatunta a makaranta.

Dalibar ta je makaranta da wani kitso ne wanda ya keta dokar makarantar, ta fuskanci horo mai tsanani a makarantar, lamarin da yasa taje kotu.

Ado-Ekiti, Ekiti – Gift Agenoisa, dalibar JSS1 a makarantar sakandare ta Mary Immaculate dake Ado-Ekiti ta maka gwamnatin jahar Ekiti a gaban babbar kotun jahar tana bukatar gwamnatin ta biyata naira miliyan 15 sakamakon shiga hakkinta na ‘yar adam.

Korafin nata mai lamba HAD/01/CR/2021 wanda Odunayo Agenoisa ya gabatar ga babbar kotun Ado-Ekiti a maimakonta, wanda dalibar tayi ikirarin dakatar da karatunta da gwamnatin tayi ya shiga hakkinta na bil’adama.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a takardar ta bayyana irin cutarwa da zaluncin da aka mata, akan zuwanta makaranta da wani kitso wanda suke ganin bai dace ba.

Su waye dalibar ta kai kara?

A cikin korafinta ta sanya Shugaban makarantar, Mrs Oluwasanmi F.M, kwamishinan ilimin jahar, Dr Olabimpe Aderiye, shugaban malaman jahar da kuma gwamnatin jahar.

A takardar kotun data hada ta bayyana yadda aka kira ta gaban gaba daya daliban makarantar a ranar 22 ga watan Mayu sannan aka yi mata bulalai 20 bisa umarnin shugaban makarantar.

A asalin takardar da lauyanta, Mr Timmy Omotoso ya gabatar, ya kawo dokoki kwarara na 1,3,4,5 da 6 na hakkin bil’adama na 2009 wadanda sashi na 315 suka gabatar daga kundin tsarin mulkin 1999, ta bukaci naira miliyan 15 akan dakatar da karatunta da sukayi.

Wanne mummunan hali dalibar ta shiga bayan dukan?

Yarinyar ta bayyana yadda ranar da ta sha dukan ta samu miyagun raunuka wadanda sai dai ta tafi kabarinta da tabo, jini yayi kaca-kaca da suturarta sannan ta suma take a wurin kafin aka wuce da ita asibitin ‘yan sanda dake Ado-Ekiti, inda aka duba lafiyarta.

Ta kara bayyana yadda wasikarta ta korafi wacce ta tura wa matar gwamna da sauran masu fadi a ji a jahar ta tashi a tutar babu.

Tace yanzu haka an hana ta zuwa ko harabar makarantar bisa umarnin shugaban makarantar tun a lokacin.

A ranar 22 ga watan mayu, mahaifin yarinyar da wani dan sanda, Elijah, suka gayyaci wasu ‘yan sanda hudu suka ci mutuncin wasu malaman makarantar akan abinda aka yi wa diyarsa akan kitson da suka ce bai dace da tsarin makarantar ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here