Bayan watanni 7: Daliban Jami’ar Gusau Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga
Jihar Zamfara – Dalibai da malaman jami’ar tarayya ta Gusau (FUG) sun shaki iskar yanci bayan shafe akalla watanni bakwai a hannun yan bindiga.
A watan Satumba, 2023 ne yan bindigiar su ka kai mummunan hari jami’ar tare da sace wasu daga cikin malamai da daliban makarantar.
Zagazola Makama, masanin tsaro a kasar nan ya wallafa a shafinsa na X cewa ya bayyana cewa dukkanin wadanda aka kwashe a wancan harin sun dawo gida.
Yadda aka sace yan jami’ar Gusau
Read Also:
Jaridar Punch ta wallafa cewa wani Abubakar Sani, mazaunin kauyen Sabon Gida a Zamfara ya bayyana cewa yan bindiga sun kutsa wurin kwanan dalibai a jami’ar FUG.
Ya kara da cewa an shiga wuraren kwanan dalibai har guda uku da 4.00n.s, inda su ka kwashi wadanda tsautsayi ya rutsa da su zuwa daji.
Mutanen Gusau sun shaki iskar yanci
Rahotanni sun tabbatar da cewa dukkanin malaman jami’ar tarayya ta Gusau da sauran wadanda aka kwashe watanni bakwai da su ka wuce sun samu yanci.
Amma ba a tabbatar da yadda aka ceto daliban da malamansu ba, ko an biya yan bindiga kudin fansa ko kuma iya kokarin jami’an tsaro ne ya kubuto da su.