ɗaliban FGC Yauri Guda 2 Sun Tsere Daga Hannun ‘Yan Bindiga
Wasu ɗalibai guda biyu daga cikin waɗanda aka sace a FGC Yauri, jahar Kebbi sun kubuta daga hannun yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa an gano ɗaliban ne a dajin Ɗansadau dake jahar Zamfara.
Tun mako shida da suka gabata, wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗalibai da dama a FGC Birnin Yauri.
Yauri, Kebbi:- Wasu ɗalibai biyu daga cikin waɗanda aka sace a makarantar sakandire a jahar Kebbi sun tsero daga sansanin yan bindiga, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Read Also:
Ɗaliban biyu, mace da namiji, suna daga cikin gomman da yan bindiga suka sace a sakandiren gwamnatin tarayya (FGC) Yauri, jihar Kebbi. Rahoton channels tv ya nuna cewa jami’an yan sanda ne suka gano ɗaliban a dajin Dansadau, ƙaramar hukumar Maru, jahar Zamfara.
Kakakin hukumar yan sanda ta jahar Zamfara, SP Muhammed Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Gusau ranar Lahadi.
Yace: “An gano ɗaliban su biyu suna yawo a dajin yankin Ɗansadau, ƙaramar hukumar Maru a jahar Zamfara.”
Shin an biya kuɗin fansa? Babu wani cikakken bayani ko an biya kuɗin fansa domin kubutar da ɗaliban yayin da ake tantama kan ragowar mutum nawa ne a hannun ɓarayin.
Mako shida da ya gabata ne wasu yan bindiga suka mamaye makarantar FGC Yawuri, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da dama tare da malamai huɗu.
A lokacin harin, yan bindigan sun kashe wani jami’an hukumar yan sanda guda ɗaya.
Sace mutane domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare a jahohin Zamfara, Kebbi da sauran jihohin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.