Manyan Dalilai 4 da Yasa ‘Yan Boko Haram Suka Ajiye Makamansu
Da alama lokaci ya kure wa mayakan Boko Haram a cikin yankin arewa maso gabashin Najeriya yayinda da yawa daga cikinsu ke karbar shirin afuwa.
Wannan na zuwa ne makwanni bayan manyan bama-bamai da sojojin Najeriya suka saki a maboyarsu daban-daban da ke warwatse a fadin yankin.
Yanzu a kulla yaumin ‘yan Najeriya na farkawa da labarin cewa da dama daga cikin ‘yan ta’addan na fitowa daga sansaninsu don mika wuya.
FCT, Abuja – A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, ‘yan ta’addan Boko Haram da dama sun mika wuya, tare da iyalansu, suna masu ajiye makamansu.
Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya na ta mamakin dalilin da yasa mayaƙan suka canza tunaninsu kwatsam bayan kusan shekaru goma suna kai farmaki ga sojojin Najeriya da ‘yan ƙasa da basu ji ba basu gani ba.
Legit.ng ta hada dalilai hudu da suka sa yan ta’addan ke yin kasa a gwiwa
1. Raguwar ƙarfi
Cewa an ƙasƙantar da mayakan Boko Haram gaba ɗaya kuma ba sabon labari bane batun durkushewar darajarsu.
Read Also:
Sojojin Najeriya a cikin ‘yan watannin da suka gabata, sun yi ruwan bama -bamai a maboyarsu tare da yi wa dakarunsu rugu -rugu. Haka yake cewa da yawa daga cikin mayaƙan za su saduda sannan kuma su fito daga maboyarsu tare da mika wuya.
2. Mutuwar Abubakar Shekau
A watan Mayun 2021, faifan muryar da kamfanonin labarai suka samu ya nuna cewa shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu ta hanyar danawa kansa bama -bamai bayan wani fada tsakanin kungiyarsa da kungiyar Islamic State West Africa (ISWAP).
Mutuwar Shekau ya sa da yawa daga cikin mayakan Boko Haram sun yi kasa a gwiwa a yakin da suke yi da hukumomin Najeriya.
3. Afuwa ga ‘yan Boko Haram
Gwamnatin Najeriya, ta Hedikwatar Tsaro, ta kaddamar da Operation Safe Corridor (OSC) a shekarar 2016. Shirin na OSC wata hanya ce ta yaki da ta’addanci da nufin gyara tubabbun mayakan Boko Haram da sake mayar da su cikin al’umma. Shirin gyaran, ya zuwa yanzu, ya gyara fiye da tsoffin ‘yan Boko Haram 2,000 tun daga shekarar 2019.
4. Yunwa
Boko Haram ta sha fama da matsalar abinci da ta haifar ta hanyar tayar da kayar baya. A cikin lokutan baya -bayan nan, maimakon kona gidaje wanda ya kasance tambarinta a yayin farmaki, mayakan suna tara shanu, awaki, da kowane irin abinci da za su iya tarawa su gudu da su.
Wannan ya biyo bayan mamayar da take kaiwaa garuruwa cikin shekaru da yawa, wanda ya tilasta mutane sama da miliyan biyu barin gidajensu da gonakinsu.