Dalilan da Yasa Gwamnatin Tarayya Zata Ciyo Bashi Daga ƙasar Brazil

Ministr kudi, zaonab Ahmed, ta ce Najeriya ta nemi sabon basshin Dalar Amurka biliyan biyu daga kasar Brazil.

Zainab ta ce gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin kudaden ne domin farfado da masana’antun cikin gida .

‘Yan Najeriya da dama na korafin cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Buhari ta na tarawa Najeriya dumbin basuka Gwamnatin na shirin rancen ƙuɗi kimanin Dala biliyan 1.2 daga ƙasar Braziƙ don bunƙasa harkar noma.

An turawa majalisa kudiri don ta sahale a ciyo bashin daga kasar Brazil. Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ce ta bayyana hakan jim kaɗan bayan ta bayyana a gaban kwamitin kuɗi na majalisar wakilai a Abuja ranar Talata don kare kasafin kuɗin ma’aikatar ta.

Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta turawa majalisa kudirin neman yarjewarta domin karɓo bashin kudaden daga kasar Brazil.

Zainab Ahmad tace gwamnatin tarayya zata mallaki hekta dubu ɗari 100,000 na gona a kowacce jiha don noman abinci.

Inda ta ƙara da cewa za’a yi titunan da zasu sauƙaƙa wajen tafiyar da kayayyakin gona don rage yawan asarar da manoma keyi bayan girbe amfanin gona.

Shugaban kwamitin ya Mr James Feleke ya tambayi Zainab Ahmad game da yadda tsarin yake. Da take bashi amsa, Zainab Ahmad ta ce; “za mu yi amfani da bashin don inganta masana’antu da muke dasu.

“Ina neman amincewarku don karɓo bashi da muke kira Green Imperative Programme, wanda ya kai kimanin Dala biliyan $1.2. “Tsari ne wanda zai taimaki harkar noma tun daga Kayan aiki, nomawa, sarrafawa da kuma siyarwa.

“Tsari ne da za’a bawa ƴan kasuwa da manoma bashi don sayen motocin noma da sauran kayan aikin shuke-shuke da kuma yin noma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here