Dalilan da Yasa Shugaban INEC ya Sauka Daga Kujerarsa
Mahmood Yakubu ya ce ya sauka daga matsayin Shugaban INEC ne domin zai zama ba “daidai” ba idan ya ci gaba da zama a ofis.
Shugaban hukumar zaben ya kuma bayyana cewa yana jiran majalisar dattawa ta sake tabbatar da shi domin ya ci gaba da ayyukansa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Yakubu a karo na biyu, wanda hakan ya sa ya zamo Shugaban INEC na farko da zai dawo a zango na biyu Daga karshe, Mahmood Yakubu, Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ya bayyana dalilinsa na mika mulki ga Muazu Ahmed duk da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada shi a karo na biyu.
Read Also:
Da yake magana a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, a hedkwatar INEC da ke Abuja, Shugaban hukumar zaben ya ce “zai zama ba daidai ba” ci gaba da aiki ba tare da majalisar dattawa ta tabbatar da shi ba.
Shugaba Buhari ya sake nada Yakubu a matsayin Shugaban INEC na wasu shekaru biyar masu zuwa a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba.
Da yake mika jagorancin INEC ga Ahmed, Yakubu ya jaddada cewa ya zama dole a bi ka’idar kundin tsarin mulki tare da yi masa biyayya, kuma ma ya ajiye aikin ne na wucin gadi.
Ya bayyana cewa har zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta tabbatar da shi, zai janye daga kasancewa Shugaban hukumar zaben Najeriya, Channels TV ta ruwaito.