Dalilin da Yasa Na Canza Jam’iyya – Abdul’aziz Nyako
Tsohon sanatan Adamawa, Abdul’Aziz Nyako, da sauran ‘yan jam’iyyar ADC na jihar sun koma APC.
A cewarsa, sun lura da yadda jam’iyyar APC take tafiyar da lamurranta cikin kwanciyar hankali.
Ya ce sai da suka tattauna da masu ruwa da tsakin jam’iyyar tukunna suka yanke wannan shawarar.
Tsohon sanatan Adamawa, Abdul’Aziz Nyako, da sauran mambobin ADC na Adamawa sun koma APC, jaridar Newswire ta wallafa.
Nyako ya sanar da manema labarai cewa, bayan shugabannin APC da na ADC sun tattauna, “Mun yanke shawarar yin maja da APC.”
Read Also:
Wannan cigaban ya biyo bayan wani gagarumin taro da masu ruwa da tsakin jam’iyyar ADC da na APC suka yi a jihar Adamawa.
“Mun ga yanayin jajircewa da dagewa wurin yin shugabancin APC, sai muka yanke shawarar angulu ta koma gidanta na tsamiya, wato mu koma APC.
“Shugabannin jam’iyyar ADC za su tattauna a kan wannan majar ga hedkwatar jam’iyyar ta kasa, don yin mai yuwuwa,” a cewarsa.
Nyako, wanda yazo a matsayi na 3 a zaben sanatocin ya bayar da tabbacin cewa sun bai wa jam’iyyar PDP ta jihar Adamawa damar tafiyar da mulkinta cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma sun gane cewa sun fi dagewa wurin siyasa a kan mulki.
“Sun samar da siyasa mara karfi ta yadda karamar iska ta isa ta zubar da jam’iyyar, don haka mun dawo APC, sannan kwanan nan za mu haska a jihar Adamawa,” a cewarsa.