Dalilin da Dakatar da Rotimi Amaechi
Tsagin jam’iyyar APC na jihar Rivers da ke yi wa Aguma biyayya ta dakatar da ministan sufuri Rotimi Amaechi.
A cewarta, ta dakatar da Amaechi ne bisa zarginsa da ake yi na aikata ayyukan cin amanar jam’iyya.
An cimma wannan matsayar ne bayan shugabannin kwamitin wucin gadi na tsagin sunyi taro don tattauna kan shawarar da kwamitin ladabartarwa ta bada kan Ameachi.
Tsagin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Igo Aguma ke jagoranta a jihar Rivers ta dakatar da ministan sufuri kuma tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Ameachi daga jam’iyyar.
Hakan na zuwa ne bayan rikicin jam’iyyar APC na jihar Rivers ya kazanta a yayin da bangarorin biyu ke kokarin karbe ikon juya jam’iyyar a yayin da babban zaben 2023 ke gabatowa, The Nation ta ruwaito.
Read Also:
Tsagin Ameachi na jam’iyyar APC a karshen mako ta dakatar da Senata Magnus Abe, Igo Aguma, Livingstone Wechie, Wogu Boms da dukkan yan kwamitin wucin gadin da Aguma ya nada.
Aguma cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Livingstone Wechie ya fitar ya kuma ce APCn ta rubuta wa hukumar zabe ta jihar, RISEC wasika tana mai cewa ta shirya shiga zaben kananan hukumomi mai zuwa.
Wechie ya ce sun cimma matsayan dakatar da Ameachi ne a yayin taron shugabanin jam’iyyar da suka yi a karkashin jagorancin Aguma a Fatawal, babban birnin jihar.
Ya ce manyan yan jam’iyyar sun hallarci taron a zahiri da kuma wadanda suka hallarta ta amfani da fasahar bidiyo da sauti na intanet.
Sanarwar ta ce kwamitin shugabannin wucin gadi na jam’iyyar sun cimma matsayar dakatar da Ameachi bayan kwamitin ladabtarwa ta jam’iyyar ta bada shawaran yin hakan duba da zargin ayyukan cin amanar jam’iyya da ake zarginsa da aikatawa.