ASUU: Dalilin Janye Yajin Aiki
Kungiyar ASUU ta fito ta bayyana dalilanta na janye yajin-aiki a Najeriya.
Shugaban kungiyar ya ce za su zubawa gwamnati ido su ga gudun ruwanta.
Biodun Ogunyemi yace za su koma idan gwamnati ta gagara cika alkawari.
A ranar Laraba ne kungiyar ASUU ta malaman jami’an gwamnatin Najeriya ta bada sanarwar janye yajin-aikin da ta dauki tsawon lokaci ta na yi.
Da ta ke magana da ‘yan jarida a jami’ar tarayya ta Abuja da ke Gwagwalada, Daily Trust ta rahoto kungiyar ASUU ta na yabon jajircewar ‘yan makaranta.
Kafin ASUU ta dakatar da wannan dogon yajin-aiki, sai da ta tabbatar an fara biyan malaman jami’a bashin wasu daga cikin bashin albashin da su ke bi.
Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu malaman jami’ar Ahmadu Bello University da ke Zaria, inda su ka tabbatar mata da cewa an biya su albashin watanni biyu.
Read Also:
Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce daga ranar 24 ga watan Disamba, za a janye yajin-aikin, amma kungiyar za ta iya komawa yajin idan aka saba alkawari.
Shugaban na ASUU ya ce majalisar koli ta NEC za su cigaba da lura da gudun ruwan gwamnatin tarayya, su tabbatar an cika duka yarjejeniyar da aka yi.
Haka zalika ASUU ta yi kira ga gwamnati ta yi maza ta kammala binciken manhajar UTAS da su ka kawo, sannan a saki kudin gyaran jami’o’in gwamnati.
Malaman jami’ar sun hakura da yajin-aikin ne bayan alkawarin za a biya su alawus din EAA, sannan nan gaba za a rika ware kudin daga kasafin kasa.
Idan ku na biye da mu, kun san cewa kungiyar malaman ta dauki matakin janye yajin-aikin na ta ne bayan an dade ana tattaunawa da gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da Duniya cewa sun dakatar da yajin-aikin bayan yin la’akari da wasu abubuwa da-dama.
Biodun Ogunyemi ya ce sun duba halin da ‘daliban kasar su ka shiga a dalilin wannan yajin-aikin.