Jahar Niger: Dalilin Rage Kudin Ma’aikata
A ranar Laraba ne kafafen yada labarai suka sanar da cewa gwanatin jihar Neja ta zabge albashin ma’aikata da kaso 50.
A cikin wani jawabi da kwamshinan yada labari na jihar ya fitar, ya bayyana dalilan daukan wannan mataki.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati za ta mayar wa ma’aikata kudadensu da zarar komai ya daidaita.
A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Niger ke yi na tattara haraji da kuɗaɗen shiga,gwamnatin jihar Niger ta fara sauye sauye kan tsare tsaren kuɗaɗen shiga da fasahar zamani.
Wannan yunƙuri anyi shine don bunƙasa lafiya da walwalar gwamnati yadda zata kawo cigaban da al’umma ke buƙata.
Daɗin daɗawa gwamnatin jihar ta ninka ƙoƙarinta don ganin ta tattara kudaɗen haraji tare da dakatar da hanyoyin zurarewar harajin.
Wannan yana cikin sauyin kwanan nan da aka yiwa dokokin tattara haraji da kuɗaɗen shiga wadda jihar ƴan majalisar jihar suka sawa hannu kuma Mai girma gwamna, Abubakar Sani Bello, ya amimce.
Gwamnatin jiha, kamar sauran jihohin Najeriya, ta samu naƙasu a kuɗaɗen shigarta da gwamnatin tarayya ke warewa jihohi (FAAC) da kuma IGR sakamakon matsin tattalin arziƙi da ƙasar ta faɗa.
Read Also:
Duk da tsawon lokacin da aka ɗauka kafin gwamnatin Najeriya ta sanar da faɗawarta matsin tattalin arziƙi, gwamnatin Najeriya ta cigaba da tattala biyan cikakken kuɗaɗen albashin ma’aikatanta na watanni banda na watan Yuni 2020.
Lamarin ya kara tabarbarewa a wannan watan, wanda hakan ya jawo wa jihar Neja samun gibin biliyan daya daga kunshin kason da ke shiga aljihunta daga FG tun daga watan Satumba.
A bangare guda kuma rashin tsaro ya na kara lashe ‘yan kudaden da jiha ke samu, saboda akwai bukatar samar da kayan aiki ga jami’an tsaro.
Hakan ya saka gwamnati cikin tsaka mai wuya; shin gwamnati Za ta iya jingine bukatar samar da tsaro, wanda hakan shine kashin baya kafa ta?
Wannan dalilin da kuma halin matsin tattalin arziki da aka shiga sakamakon gurguncewar samun kudin shiga, su ne suka tilasta gwamnati ta zabge albashin watan Nuwamba domin gudanar da wasu muhimman aiyuka.
Wadannan bayanai sun fito ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Muhammad Sani Idris, ya fitar ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba.
A cewar kwamishinan, zabge albashin ya shafi har gwamna da mataimakinsa da sauran nadaddu da zababbun da ke rike da mukaman siyasa.
Idris ya ce suna fatan al’amura Za su sauya, su farfado, nan bada dadewa ba, inda ya bayyana cewa gwamnati Za ta mayar wa da ma’aikata kudinsu da zarar komai ya koma saiti.