Ko Menene Dalilin da Yasa Tambuwal ya Janyewa Atiku ?

Bayanai sun fito kan ainahin dalilin da yasa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben fidda gwanin PDP.

Mai magana da yawun kungiyar kamfen din Tambuwal, Prince Daniel, ya ce gwamnan na jihar Sokoto ya janyewa Atiku ne saboda kishin kasa da son ci gaban Najeriya.

Atiku dai ya yi nasarar mallakar tikitin takarar shugaban kasa na PDP bayan Tambuwal ya janye masa sannan ya samu kuri’u 371

Kakakin kungiyar yakin neman zaben Tambuwal, Prince Daniel, ya bayyana dalilan da suka sa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a yayin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP.

Legit.ng ta rahoto cewa bayan janye masa da Tambuwal ya yi, Atiku ya lashe zaben da kuri’u 371 inda ya kayar da babban abokin takararsa Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers wanda ya samu kuri’u 237.

Daniel, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce Tambuwal ya janye ne saboda kishin kasa da son ganin ci gaban Najeriya, jaridar The Punch ta rahoto.

Sanarwar ta ce:

“Hukuncin Tambuwal na janyewa daga tseren duk da cewar shi ke da damar mallakar tikitin ya kasance ne saboda tsananin sonsa ga Najeriya musamman ma ga jam’iyyar.

“Zuwa ga tarin magoya bayanmu, muna so ku sani cewa mun dauki wannan hukuncin ne saboda kishin kasa, inda muka sanya kasarmu Najeriya da jam’iyyarmu sama da ra’ayin kanmu wanda muka nanata cewa bai kai ra’ayin kasarmu ba.

“Mai girma gwamna na matukar godiya ga shugaban kungiyar kamfen dinsa kan kyakkyawan jagorancinsa, da daukacin tawaga da dukkanin deleget da dimbin magoya bayansa a fadin kasar nan kan goyon bayansu gare shi kafin babban taron, da yayin taron da kuma bayan taron.

“Ya roki Allah ya yiwa PDP jagora da bata nasara yayin da jam’iyyar ke aiki don ceto Najeriya daga mulkin kama karya na tsawon shekaru da gwamnatin APC ta yi.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here