Dalilin da Yasa Muka Tsare Shugaban NLC, Joe Ajero – Ƴan Sanda
Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Imo ta musanta rahotannin da ke zargin jami’anta da kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajero a garin Owerri.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a jihar Imo, ASP Okoye Henry, ta ce ta tafi da shi ne “domin tsare rayuwarsa”.
Sai dai ƙungiyar ƙwadagon ta ce jami’an tsaro sun kama shugaban nata ne bayan ya isa jihar ta Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Read Also:
“Daga cikin abubuwan da Mista Ajaero ya je yi Imo akwai shirya babbar zanga-zanga da tsayar da aiki cak a filin jirgin sama, kuma a wajen yunƙurin yin hakan ne wasu ma’aikata suka nuna rashin amincewa kuma wani dandazon jama’a ya kai masa hari,” in ji ASP Henry.
“Bayan mun samu labari, sai rundunar ‘yan sandan Imo ta tura dakarunta kuma jagoran tawagar ya ɗauki shugaban na NLC zuwa hedikwatarta don tabbatar da kare rayuwarsa daga maharan.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “daga nan sai kwamishinan ‘yan sanda ya bayar da umarnin kai shi asibitin ‘yan sanda don duba lafiyarsa…kuma aka ba shi cikakken tsaro don ci gaba da harkokinsa”.
Sai dai kuma, rundunar ta jaddada cewa ya kamata a yi la’akari da hukuncin kotun ɗa’ar ma’aikata da ta hana NLC gudanar da zanga-zangar a ranar 27 ga watan Oktoba.